12 Nuwamba 2016 - 16:54
An Wargaza Wata Kungiyar Yan Ta'adda A Kasar morocco

Ma'aikatar harkokin cikin gida na kasar Morocco ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar wargaza wata kungiyar yan ta'adda a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya nakalto ma'aikatar cikin gidan na kasar ta Morocco tana fadar haka a jiya Jumma'a, ta kuma kara da cewa kungiyar yan ta'addar mai mutane hudu ne, kuma tun da dadewa jami'an tsaron kasar sun lura da kai kawain mutane biyu daga cikinsu kan dandantakansu da kungiyoyin yan ta'adda a kasashen waje, wadanda suka hada da Iraqi da Siria. Har ma an taba dauresu kan hakan. a yayinda daya daga cikinsu kuma yake karkashin kula na jami'an tsaron kasar dangane da fasa korin miyagon kwayoyi , banda haka a shekara ta 2014 ne ya dawo daga kasar Beljika.

Labarin ya kara da cewa Jami'an tsaron sun rutsa da su a garuruwan Tanja daga arewacin kasar da kuma Wajda daga arewa maso gabacin kasar.288